Hukumar gudanarwar tarayyar Turai ta ci tarar kamfanin Apple dala biliyan 2 kan karya dokokin kare masu amfani da wayoyin a Turai.
Shugabar hukumar da ke sa ido kan gogayya tsakanin kamfanoni Margrethe Vestager, ta ce a tsawon shekaru kamfanin ya yi amfani da damarsa ta kasancewa mafi shahara wajen hana mutane su san cewa akwai masu manhajoji masu samar da waƙoƙi a farashi mai rahusa.
Karin labari: Kotun kolin Amurka ta ki amince yunkurin cire Trump daga zabe
“Ya zama dole mu sa ido kan kamfanoni irinsu Apple da ke karya dokokin kare masu amfani da wayoyin a Turai,” in ji Vestager.
Ta kuma umarci kamfanin na Amurka ya cire duk wasu shingaye da yake sawa domin ganin masu amfani da wayoyinsa walwalawa. Sai dai kamfanin Apple ya ce zai daukaka kara.