Sanata Dakta Babangida Hussaini Walin Kazaure, ya bukaci ‘yan Najeriya da su kasance masu da’a tare da fatan samun ingantacciyar rayuwa a kasar nan.
Ya bayyana hakan ne a cikin sakonsa na sabuwar shekarar 2024 ga al’ummar santoriyar Jigawa ta arewa maso yamma.
Karanta wannan: Kakakin Majalisar Ribas Rt. Hon Edison Ehie ya yi murabus
Walin Kazaure ya ce duk da kalubalen da ake fuskanta na zamantakewa da tattalin arziki a yanzu, matukar ‘yan Najeriya suka hada kai tare da yin addu’o’I za’a samu kyakyawar makoma.
Karanta wannan: Gwamna Namadi ya jaddada aniyarsa ta bunkasa Ilimi da Lafiya a Jihar Jigawa
Yace sabuwar shekarar ta sake bada damar tunkarar kalubalen tsaro a kasar nan da farfado da tattalin arziki da sanya matasan kasar nan a gaba, da kuma sauran abubuwan da za su kai kasar nan ga tudun mun tsira.
“Da yardar Allah za mu iya shawo kan kalubalen dake addabar al’ummar mu, zamu tsaya tsayin daka wajen yin abubuwan da suka dace.” Inji Wali.
Karanta wannan: Kano: Gwamna Yusuf da mataimakinsa sun gudanar da bikin sabuwar shekara ta 2024
A cewarsa a wannan shekara ta 2024 yana da burin dorawa akan ayyukan ci gaban daya faro a shekarar 2023, musamman abubuwan da ya fi bawa fifiko a mazabarsa.
Abubuwan da ya fi maida hankali akai, sune bangaren ilimi da samar da guraben aikin yi ga matasa, baya ga samar da ruwan sha mai tsafta da kuma bunkasa harkokin kiwon lafiya a yankin.