Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya sake jaddada cewa gwamnati ba za ta lamunci rashawa ko cin hanci ba, inda ya yi kira ga matasa da su shiga gaba wajen yaki da rashawa domin gina makoma mai gaskiya da wadata ga jihar.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Talata yayin wani taron bita da aka shirya domin tunawa da Ranar Yaki da Rashawa ta Duniya ta 2025, wanda Hukumar Korafe-Korafe da Yaki da Rashawa ta Jihar Kano ta tsara.
Gwamna Yusuf, wanda Sakataren Gwamnatin Jihar, Malam Umar Farouk ya wakilta, ya ce taken taron na bana an yi masa take da “Hadin kai da matasa wajen yaki da rashawa: Gina gaskiya don gobe” ya yi daidai da manufofi da alkiblar gwamnatin sa.
Ya kara da cewa rashin kasancewarsa a wurin taron sakamakon wasu ayyukan hukuma a Abuja da Legas ya sa ba zai kasance tare da mahalarta ba, sannan yana da cikakken goyon baya ga manufar.
Gwamna Yusuf ya jaddada cewa gwamnatin sa ta zo ne don sake gina tsarin yaki da rashawa da kuma dawo da cikakken ‘yanci da ikon gudanar da ayyuka ga Hukumar Korafe-Korafe da Yaki da Rashawa ta Jihar Kano.
Jaridar Solacebase ta rawaito cewa gwamnan ya bayyana shirye-shiryen horar da ma’aikatan siyasa da manyan jami’an gwamnati kan gaskiya da yadda za a sarrafa albarkatun jama’a cikin hikima, domin tabbatar da shugabanci mai nagarta a dukkan bangarorin gwamnati.
Ya lissafa nasarorin da aka samu wajen kare dukiyar jama’a, ciki har da dawo da filaye da kadarorin da aka kwace, ayyana dokar ta-ɓaci a fannin ilimi, farfado da inshorar lafiya, biyan bashin fansho da alawus-alawus, da sabunta zuba jari a fannin noma, lafiya da ababen more rayuwa.
A nasa bangaren shugaban Hukumar Korafe-Korafe da Yaki da Rashawa ta Jihar Kano (PCACC), Malam Saidu Yahya, ya bayyana ranar a matsayin mai tarihi ga hukumar, inda ya nuna kokarin sabunta hadin gwiwa da matasa wajen yaki da rashawa.
Karanta: Gwamnan Kano ya gabatar da Naira Tiriliyan 1.368 a matsayin kasafin kuɗin shekarar 2026 ga majalisa
Ya ce hukumar ta fahimci cewa ba za ta iya cimma burinta kadai ba, don haka akwai bukatar aiki tare da duk masu ruwa da tsaki, musamman matasa wadanda su ne “makomar gobe” kuma mafi mutuwa da sakamakon rashawa.
Yahya ya bayyana cewa tun bayan karbar ofis a watan Agusta 2025, ya yi kokarin karfafa ikon gudanar da ayyukan hukumar bisa gogewar sa na shekaru 18 a ICPC, inda ya kawo sabbin hanyoyin aiki da dabarun da ake amfani da su a matakin tarayya domin inganta aikin hukumar.
Babbar Alkaliyar Jihar Kano, Mai Shari’a Dije Aboki, wanda mai Shari’a Jamilu Yusha’u ya wakilta, ya isar da sakon alheri daga bangaren shari’a ga mahalarta taron.
Ya jaddada cewa yaki da rashawa na bukatar sadaukarwa, jajircewa da dagewa, sannan ya nuna cewa shari’a na shirye ta hada kai da bangarorin zartarwa da dokoki wajen yakar rashawa.
Ya bayyana fatan cewa matasa mahalarta taron za su kasance shirye su jagoranci canjin al’umma da kuma zama zakaran gaskiya a hidimar gwamnati.













































