Gwamnan jihar Osun  ya koma jam’iyyar Accord Party

WhatsApp Image 2025 12 09 at 19.46.49 38d21bc7 750x536 1 750x430

Gwamnan jihar Osun Ademola Adeleke ya sanar da komawarsa jam’iyyar Accord Party domin neman wa’adi na biyu a zaben watan Agusta na badi.

Gwamnan ya bayyana wannan mataki ne a dakin taro na Banquet Hall da ke fadar gwamnatin Osogbo, tare da shugabannin jam’iyyar na kasa da na jiha.

Adeleke ya bayyana cewa ya shiga jam’iyyar ne tun ranar 6 ga Nuwamba bayan shawarwari da tattaunawa da masu ruwa da tsaki, domin samun sabon dandali na neman ci gaba da mulki a 2026.

Ya ce shugabanni da al’ummar Osun sun san dalilan wannan mataki, yana mai bayyana cewa dacewar manufofin jam’iyyar Accord Party da manufarsa ta inganta jin dadin jama’a shi ne ya sa ya zaɓi jam’iyyar.

Gwamnan ya karɓi shugabannin jam’iyyar a gidan gwamnati na Osun, yana mai tabbatar musu da cewa suna aiki tare domin ci gaba da samar da kyakkyawan shugabanci a fadin jihar.

Adeleke ya yi bayanin cewa ya fahimci manufar jam’iyyar tun lokacin da ya shiga cikinta, yana mai cewa jagoranci dole ya kasance kan jin dadin al’umma da kare muradunsu a dukkan yankunan jihar Osun.

Shugaban jam’iyyar na kasa Maxwell Mgbudem ya tarbi gwamnan cikin jam’iyyar, tare da tabbatar masa da cikakken goyon bayan jam’iyyar a shirin da ake yi na fita takara a zaben shekara mai zuwa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here