
Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta ce ba ta da masaniyar inda dakataccen Kwamishinan Zabe na Jihar Adamawa Hudu Ari yayi, tun bayan dambarwar da ya yi a lokacin zaben cike gurbin Gwamna a Jihar Adamawa.
Ari ya jawo cece-kuce lokacin da ya bayyana zaben cike gurbi a sakamakon zaben gwamna a jihar Adamawa a ranar Lahadin da ta gabata yayin da ba a kammala tattara sakamakon zaben ba.
“Yayi batan dabo, Ba mu san inda yake ba, domin bayan faruwar wannan lamari, hukumar ta rubuta masa takarda kuma ta kira shi a waya. Bai biyo kiran ba kuma bai taba amsa kiran ba.
“Mun neme shi da ya kai kan sa ga Hukumar ranar Lahadi ba mu gan shi ba, mun ce ya kawo kan sa ranar Litinin ba mu gan shi ba. Don haka har ya zuwa wannan lokaci, bai bayar da rahoto ba kuma ba mu san inda yake ba,” in ji Kwamishinan INEC na kasa Festus Okoye a ranar Juma’a a gidan Talabijin na Channels Television.
Da aka tambaye shi ko yana ganin za a ayyana Ari a matsayin wanda ake nema ruwa a jallo saboda ya kasa kai kansa ga hukumar ko amsa kiran ta, Okoye ya ce wannan nauyi ne da ya rataya a wuyan ‘yan sandan Najeriya.
Bayan dakatar da Kwamishinan, INEC ta kai karar sa ga shugaban kasa Muhammadu Buhari, wanda a ranar Alhamis din da ta gabata ya amince da dakatar da Ari, har sai an kammala bincike da Sufeto Janar na ‘yan sanda ya yi kan yadda ya tafka shirme kan sakamakon zabe.
Kwamishinan na INEC na kasa ya ce hukumar ta samu rahoto daga babban sufeton ‘yan sandan kasar, kuma ta fara aikin gurfanar da Ari.
“Mun rubutawa babban sufeton ‘yan sanda da sakataren gwamnatin tarayya. Mun samu martani daga babban sufeton ‘yan sandan kasar kuma tuni suka fara bincike.












































