Shugaba Tinubu ya dawo Najeriya bayan ziyartar kasashe – Fadar Shugaban Kasa

Tinubu, Shugaba, kasashe, Najeriya
Shugaba Bola Tinubu da mukarrabansa sun dawo Najeriya daga kasashen Turai ranar Laraba. Mai bawa shugaban kasa shawara na musamman kan yada labarai da dabaru...

Shugaba Bola Tinubu da mukarrabansa sun dawo Najeriya daga kasashen Turai ranar Laraba.

Mai bawa shugaban kasa shawara na musamman kan yada labarai da dabaru, Bayo Onanuga, wanda ya sanar da ci gaban a cikin wani sakon da ya wallafa a shafinsa na X a yau, ya yi maraba da shugaban kasar zuwa kasar.

“Barka da Dawowa Mai Girma Shugaba!” ya rubuta.

Karin labari: Hotuna: Sarkin Kano ya ziyarci Shekarau don yin jajen gobara

Shugaba Tinubu ya yi tattaki ne domin ganawa da firaministan kasar Holland, Mark Rutte, makonni biyu da suka gabata, inda ya tafi kasar Saudiyya don halartar wani taron tattalin arziki na musamman na duniya (WEF).

Daga baya ya tafi Turai bayan taron.

Idan dai ba a manta ba a ranar 22 ga watan Afrilu shugaban yabar Abuja zuwa kasar Netherlands a wata ziyarar aiki da ya kai kasar.

Karin labari: Gwamnan Kano ya rattaba hannu kan dokar tantance lafiya kafin Aure

Kakakin shugaban kasar, Ajuri Ngelale, ya ce ya ziyarci kasar Netherland ne bisa gayyatar da firaminista Mark Rutte ya yi masa.

Bayan an gama a Netherlands, Tinubu ya zarce zuwa Riyadh a Saudi Arabia don halartar taron WEF na musamman tsakanin 28 da 29 ga watan Afrilu.

Ana sa ran shugaban ya dawo kasar bayan taron da aka yi a Saudiyya, amma bai dawo ba, lamarin da ya kara rura wutar cece-ku-ce a kan inda yake.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here