Majalisar Dattawa ta amince da dokar ta-bacin da Tinubu ya sanya a Rivers

Senate 1

Majalisar Dattawa ta amince da ayyana dokar ta-baci a jihar Rivers da Shugaba Bola Tinubu ya yi, a zaman ta na yau Alhamis.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa, a ranar Talata ne shugaban kasar ya kafa dokar ta-baci a Rivers.

NAN ta kuma ruwaito cewa sanarwar ta shugaba Tinubu ga”ta dakatar da gwamnan da mataimakiyarsa da ‘yan majalisar dokokin jihar na tsawon watanni shida.

A doka dole ne bangarorin biyu na Majalisar su amince da sanarwar a cikin kwanaki biyu na sanarwar, kamar yadda kundin tsarin mulki na 1999 (kamar yadda aka gyara), idan ba haka ba matakin ya zama rusashshe.

Amincewar majalisar dattijai a ranar Alhamis ya biyo bayan la’akari da bukatar hakan daga shugaban kasa.

Tinubu ya rubutawa majalisar dattawan cewa ta gaggauta duba batun kafa dokar ta-baci a Rivers, tare da dakatar da gwamna da mataimakiyarsa da kuma ‘yan majalisar dokokin jihar daga ofis.

Bayan karanta wasikar ta shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, da shugaban masu rinjaye na majalisar dattawan Opeyemi Bamidela (APC-Ekiti), ya gabatar da bukatar sake yin odar kayayyakin da ke cikin takardar.

Sanata Abba Moro na PDP daga Benue shi ma ya goyi bayan kudirin.

Karanta: Cikin hotuna: Ana zaman fargaba yayin da hukumar FAAN ta yi rusau a gidajen mutanen da ke zaune a Aviation Quarters na filin jirgin sama na Kano

Sai dai wani batu da ya fito daga bakin Sen. Henry Dickson (PDP-Bayelsa) ya sanya majalisar dattawa ta yanke shawarar shiga wani zama na gaggawa don tattaunawa kan lamarin.

NAN ta ruwaito cewa tun bayan kammala zaman majalisar ta amince da ayyana dokar ta baci a jihar.

Akpabio, a jawabinsa bayan kammala taron, ya ce majalisar ta yi amfani da ikonta, kamar yadda sashe na 305 (2) na kundin tsarin mulkin kasa na 1999 wanda aka yi wa gyara ya ba ta, ta kuma amince da sanarwar.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here