Babban mai goyan bayan Yemi Osinbajo ya yiwa Tinubu murna

Tinubu speaking
Tinubu speaking

Babban mai goyan bayan mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo, Richard Akinnola ya yiwa tsohon gwamnan jihar Lagos,  Bola Ahamad Tinubu murna a shafin sa na sada zumun ta.

Yanzu haka dai Tinubu ne ke kan gaba da kuri’u  890, sai kuma takwaran sa, Rotimi Amaechi da ke biye masa baya, yayin da kuma Yemi Osinbajo ke biye wa Amaechi.

Amaechi dai yasami adadin kuri’u 175 ya yin da mataimakin shugaban kasa Buhari keda da kuri’u 126.

Akinnola ya ce duk da cewa dukkanin alamu sun nuna cewa Tinubu ne zai lashe zaben fitar da gwani na  jam’iyyar APC, amma ya ce yana alfahari da zamowar sa babban magoyin bayan Osinbajo.

Adadin daliget din APC da suka kada kuri’u a zaben fitar da gwani da yake gudana yanzu haka a filin wasa na Eagle Square Abuja ya kai 2,260

Kididdiga ta adadin daliget din jihahohin Najeriya  da aka tantan ce ta nuna cewa Abiya na da 50; Adamawa na da 62; Anambara na da 63; Bayalsa na da 24; Bauchi na da 55; Benue na da 64; Borno na da 81; Cross River na da 54; Delta na da 73; Enugu na da 51; Ekiti na da 48; Edo na da 54; Ebonyi na da 38;  sai FCT na da 80.

Sauran jihahohin sun hada da Gombe inda ke 33; Imo na da 81; Jigawa na da 81; Lagos na da 60; Plateau na da 51; Katsina na da 102; Kebbi na da 63; Kwara na da 48; Kogi na da 63; Kaduna na da 61; Kano na da 126; Nasarawa na da 39; Niger na da 75; Ondo na da 54; Ogun na da 60; Oyo na da 99; Osun na da 90; Rivers na da 69; Sokoto na da 69; Taraba na da 46; Yobe na da 51 ya yin da Zamfara- kuma ke da 42.

 

 

 

 

 

 

 

 

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here