Shugaban Rundunar Sojojin Saman Najeriya (CAS), Air Marshal Hassan Abubakar, ya bayar da umarnin gudanar da bincike kan mutuwar ma’aikacin wucin gadi na asibitin rundunar sojin saman ta (NAF) 465 da ke Kano, Mista Yusuf Shuaibu.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da aka rabawa kamfanin NAN wanda Daraktan hulda da jama’a da yada labarai na NAF, Air Vice Marshal Edward Gabkwet, ya fitar a ranar Talata a Kano.
Karin labari: Mutane 2 sun mutu bayan shan maganin gargajiya
“Ina sane da cewa marigayin, Yusuf Shuaibu, ma’aikaci ne na wucin gadi na Asibitin NAF 465 a Kano. Ina kuma sane da cewa kwanaki 2 da suka gabata, marigayin da wani sojan sama sun yi taho-mu-gama da ya barke kan iyaka da kuma kin bin wasu umarni da marigayin ya yi.
“Ina kuma sane da cewa bayan rikicin na su, an sasanta lamarin cikin ruwan sanyi, sannan marigayin ya koma gida ba tare da wata alamar rashin lafiya ba, sai da aka tantance washe gari cewa ya rasu.
Karin labari: Da Dumi-Dumi: Gwamnatin Adamawa ta rufe makarantu saboda bullar cutar kyanda
“Hakika, an sanar da shugaban hafsan sojin sama Air Marshal Hassan Abubakar labarin rashin tausayi da rashin jindadi na Mista Shuaibu, kuma ya yi alhinin rashin.
“Duk da haka, ya umarci kwamandojin Asibitin da NAF Base Kano da su mika ta’aziyyarsa da na dukkan iyalan NAF ga iyalan mamacin,” in ji Gabkwet.
Ya ce, saboda haka, CAS ta ba da umarnin gudanar da bincike don gano ainihin abin da ya kai ga mutuwar Mista Yusuf.
Karin labari: NCoS ta ce fursunonin Kano na da ikon ba da gudunmawa ga iyalansu daga tsare
Mutuwar Shuaibu ta haifar da bacin rai a tsakanin mazauna unguwar Gwagwarwa da ke karamar hukumar Nassarawa tare da mahaifinsa Shuaibu Bala, inda suka yi kira ga gwamna Abba Kabir Yusuf da Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero da kuma hukumar kare hakkin dan adam ta kasa. Da shugaban hafsan sojin sama ya shiga tsakani domin tabbatar da cewa iyalansa sun samu adalci kamar yadda jaridar NAN ta rawaito.