Mutane biyu ne suka rasa rayukansu a karshen mako a Ipe-Akoko da ke karamar hukumar Akoko ta Kudu maso Gabas ta jihar Ondo bayan sun sha maganin gargajiya a yayin wani bikin gargajiya da aka gudanar.
Wadanda aka bayyana sunayen sun mutu akwai Alex Ojulewa da Samuel Alonge, an ce sun mutu ne bayan sun isa wajen domin gudanar da bukukuwan gargajiya da aka fi sani da ‘Ibogbe’.
A cewar shaidun gani da ido, jim kadan bayan sun sha maganin, nan take mutanen biyu suka fara rashin lafiya tare da amai.
Karin labari: Da Dumi-Dumi: Gwamnatin Adamawa ta rufe makarantu saboda bullar cutar kyanda
Daya daga cikin wadanda suka shaida lamarin, mai suna Tunji, ya bayyana cewa, duk da kokarin garzayawa da su asibiti mafi kusa, saidai yanayinsu ya kara tsananta, wanda ya kai ga mutuwarsu kafin a kai musu dauki.
Da aka tuntubi kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Funmilayo Odunlami-Omisanya, wadda ta tabbatar da faruwar lamarin, ta bayyana cewa an fara bincike.