Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta tabbatar da cafke tsoffin jami’anta biyu Barry Donald da Victor Onyedikachi Godwin, bisa zargin Zamba da damfarar jama’a ta hanyar kwaikwayon jami’an hukumar.
Hukumar ta bayyana cewa ta taba fitar da sanarwa a baya inda ta yi gargaɗi ga jama’a cewa mutanen biyu ba sa cikin ma’aikatanta tun da an sallame su daga aiki, amma duk da haka suna ci gaba da bayyana kansu a matsayin jami’an DSS domin yaudarar mutane.
A cewar sanarwar, an kama mutanen biyu yanzu, kuma za a gurfanar da su a gaban kotu domin fuskantar hukunci bisa doka.
Wannan mataki, in ji hukumar, yana daga cikin kokarinta na tabbatar da gaskiya da bin doka a ayyukanta.
Hukumar DSS ta kuma bayyana cewa tana shirin wallafa sunayen sauran tsoffin jami’an da aka kora a baya domin hana jama’a fadawa tarkon masu yin amfani da sunan hukumar wajen aikata zamba.
Hukumar ta tabbatar da cewa tana ci gaba da aiki da ƙwarewa, gaskiya da riƙo na amana ga al’umma, tare da kira ga jama’a su kasance masu lura da duk wani motsi ko mutum da ke da shakku, su kuma kai rahoto ga ofishin hukumar mafi kusa.
Domin neman ƙarin bayani ko yin ƙorafi, hukumar DSS ta ba da lambar waya 09088373515 da adireshin imel dsspr@dss.gov.ng domin tuntuba kai tsaye.Fq
Wannan matakin ya nuna yadda hukumar DSS ke ƙoƙarin kare martabarta da hana masu amfani da sunanta wajen aikata munanan ayyuka a cikin al’umma.











































