Sojoji sun sha alwashin shafe tarihin Bello Turji 

Bello Turji

 

Babban Hafsan Tsaron Ƙasa ya bayyana shugaban ‘yan ta’adda, Bello Turji, a matsayin “mataccen mutum mai tafiya,” yana mai cewa sojoji za su ci gaba da murƙushe duk wani ɗan ta’adda.

Direktan Harkokin Yaɗa Labarai na Tsaro, Manjo Janar Edward Buba, ya bayyana hakan yayin taron manema labarai a Abuja, inda ya ce Turji da sauran shugabannin ‘yan ta’adda za su sha irin na waɗanda aka kashe a 2024.

Ya bayyana sunayen shugabannin ‘yan ta’adda da aka kashe, ciki har da Halilu Sububu da Mohammed Amadu, tare da jaddada cewa hare-haren sojoji sun tilasta wa wasu daga cikin ‘yan ta’adda mika wuya.

Buba ya ƙara da cewa sojoji za su ci gaba da kare ƙasar da cikakken ƙarfi don tabbatar da zaman lafiya.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here