‘Yan ta’adda sun yi garkuwa da jami’in Kwastam tare da iyalansa a Zariya 

Nigeria Kidnappings Bandits deputy
Nigeria Kidnappings Bandits deputy

Wasu ‘yan ta’adda a ranar Laraba da daddare sun kai hari a unguwar Low-cost a jihar Kaduna, inda suka yi awon gaba da wani Alhaji Mu’awiya Gambo Turaki tare da iyalansa.

Maharan sun mamaye garin a Kofar Gyan, Zaria, jihar Kaduna da misalin karfe 9 na dare.

Majiyoyi sun ce wanda aka sace, jami’in kwastam ne, an ce an sace shi tare da iyalansa.

“Ba a sani ba ko an hari shi ne ko kuma an yi garkuwa da shi,” daya daga cikin majiyar ta ce.

Sai dai kuma rahotanni sun ce an tattaro jami’an tsaro zuwa yankin, lamarin da ya sa ‘yan ta’addan suka tsere zuwa garin Gwargwaji.

Harin na baya-bayan nan ya faru ne a daidai lokacin da kasar ke ci gaba da kokawa da harin jirgin kasan Kaduna wanda ya afku a daren Litinin.

Har yanzu dai ‘yan sandan ba su ce uffan ba kan harin da kuma sace su

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here