Harin Jirgin Kasan Kaduna: ‘Yan ta’adda sun fara tuntubar iyalan wadanda aka sace

bomb train 2
bomb train 2

 

Wasu da ake zargin ‘yan ta’adda ne da suka kai hari kan jirgin Abuja zuwa Kaduna a ranar Litinin din da ta gabata tare da yin garkuwa da wasu da abin ya rutsa da su, sun fara tuntubar iyalansu, duk da cewa ba su yi wata bukata ba.

Solacebase ta ruwaito cewa harin da aka kai kan jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna a daren Litinin ya yi sanadin mutuwar mutane 8, wasu 26 suka jikkata, wasu da dama kuma ba a gansu ba.

Daga cikin wadanda harin ya rutsa da su akwai, Sakatare-Janar na Kungiyar Kwadago (TUC) Musa Ozigi-Lawal, Shugaban TUC reshen Jihar Kwara Akin Akinsola, Mataimakin Darakta na Hukumar Ilimin Fasaha (NBTE), Abdul Isa Kofar-Mata da kuma likitan hakori Dr Chinelo Nwando.

Har ila yau, cikin wadanda suka bace har da Manajan Daraktan Bankin noma, Alwan Hassan wanda iyalansa suka shaida wa Solacebase a ranar Laraba cewa har yanzu ba su san inda yake ba.

 

”Ko da yake har yanzu ba mu ji ta bakinsa ba amma wayarsa da aka kashe da farko a ranar Litinin da daddare ana samunta a kunne lokaci zuwa lokaci,” in ji majiyar dangin.

Wata mata mai suna Maryam Bobbo da mijinta da ‘ya’yanta an ce suna cikin wadanda suka bace a harin na jirgin kasa.

Sai dai a ranar Laraba daya daga cikin dangin Yusuf Attah, dan gidan sarautar Ohinoyo na Ebiraland, ya shaida wa Nigerian Tribune cewa an yi garkuwa da mahaifiyarsa da ‘yar uwar sa yayin harin.

Ya ce ‘yan ta’addan sun kira gidan inda ya tattauna da ‘yar uwar sa inda suka ce suna nan lafiya.

Wani dan gidan mai suna Yahaya Abdul, shi ma ya ce ‘yan bindigar sun kira shi suka shaida masa dan uwansa yana nan lafiya kuma ya jira kiran su.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here