Gwamnatin jihar Kaduna ta yi Allah wadai da kalaman tsohon gwamnan jihar Nasir El-Rufai a wani shirin gidan talabijin na baya-bayan nan, inda ya zargi gwamnatin tarayya da na jihohi da ba da kudin fansa ga yan bindiga domin a samu zaman lafiya.
A wata sanarwa da kwamishinan tsaro na cikin gida da harkokin cikin gida, Dr Suleiman Shuaibu ya fitar a ranar Litinin, ya ce kalaman El-Rufai ba magana ce kawai ba, munanan karya da aka tsara domin dakile ayyukan tsaro, tada hankalin jama’a, da kuma halasta aikata laifuka.
Sanarwar ta kuma ce, abubuwan da tsohon gwamnan ya yi a baya-bayan nan sun kasance barazana ga zaman lafiya da ci gaba kai tsaye, inda ta kuma zarge shi da shirya makarkashiyar tada zaune tsaye a jihar ta hanyar tada hankali, magudi da tunzura jama’a, inda ta yi gargadin cewa ba za ta amince da yunkurin mayar da jihar cikin tashin hankali ba.
A cewar Kwamishinan, tsohon gwamnan ya kara kaimi ne bayan da aka kayar da abokan siyasar sa a zaben da aka gudanar a ranar 16 ga watan Agusta.
“Wannan Gwamnati ba za ta nade hannunta ba, ta bar tsohon shugaban da ba a amince da shi ba, wanda ya bar jihar a ruguje, ya kunna rudani tare da jefa jihar cikin wani yanayi na rikicin kabilanci, rashin tsaro, da tabarbarewar tattalin arziki,” in ji Kwamishinan.
Gwamnatin ta kuma zargi El-Rufa’i da kiran “taron da ba bisa ka’ida ba da hargitsi” a ranar 30 ga watan Agusta, tare da abokansa na siyasa wanda ya rikide zuwa tashin hankali, ciki har da harbe-harbe da ke jefa ‘yan kasa cikin hadari.
Kwamishinan ya kuma bayyana cewa tuni ofishin mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro (ONSA) yayi watsi da zargin da El-Rufai yayi, inda yace gwamnatin tarayya ko wata hukuma dake karkashinta babu wanda ya taba biyan ‘yan bindiga kudin fansa.
A cewarsa, an ga nasarorin tsaro da aka samu a gwamnatin Gwamna Uba Sani a yankunan da ake fama da rikici a baya kamar Birnin Gwari, Giwa, Kajuru, Kauru, Kachia da Igabi. Ya ce an kawar da fitattun jagororin ‘yan fashi da suka hada da Boderi, Baleri da Sani Yellow, yayin da aka kama ‘yan kungiyar Ansaru.
Kwamishinan ya gargadi El-Rufai da ya daina ayyukan da ka iya kawo barazana ga zaman lafiya, yana mai jaddada cewa an sanya jami’an tsaro cikin shiri.













































