An kama Shugaban Hukumar Karbar Korafe-Korafe da Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Kano, Muhuyi Magaji Rimingado, bisa zargin karɓar kadarorin da ake dangantawa da tsohon gwamna Abdullahi Ganduje.
Yansanda sun kama shugaban hukumarne biyo bayan karbar umarni daga Insifecta Janar Kayode Egbetokun.
Wata majiya ta bayyanawa jaridar SolaceBase cewa a yammacin yau Juma’a ne jami’an suka dira a ofishin hukumar bisa jagorancin ASP Ahmed Bello, suna masu cewa sun karbi umarni kan kama Rimin Gado.
Majiyarmu ta rawaito cewa lamarin ya shafi shari’ar Bala Muhammad Inuwa, tsohon MD na KASCO, wanda ake tuhuma da karkatar da sama da Naira biliyan huɗu.
Hukumar ta ce ta kwace kadarorin bisa doka, amma an yi ƙoƙarin cire ‘yan sandan da ke kula da su.
Bayan kama Muhuyi, an kai shi Zone 1 a Kano, inda aka hana lauyoyinsa ganawa da shi, kuma babu martani daga ɓangaren Ganduje ko ‘yan sanda kan batun.