Muna kira ga gwamnati da ta fadakar da mambobinmu game da cutar Mashako-Jajere

IMG 20230729 WA0067
IMG 20230729 WA0067

Kungiyar Miyetti Allah Kautal Hore ta kasa reshen jihar Kano, ta bukaci gwamnatin jihar Kano da ta gudanar da gangamin wayar da kan mambobinta, game da illar sabbin cutukan da suka bulla a baya-bayan nan.

Mataimakin Shugaban kungiyar na jihar Kano Alhaji Abubakar Muhammad Jajere, shi ne ya mika wannan bukatar a zantawarsa da manema labarai, inda yace sun sami labarin bullar wata sabuwar cutar ma ta dabbobi daga daga kasar Ghana, adon haka suke bukatar gwamnati ta bada gudanarwa wajen fadakar da mambobinta musamman wadanda suke zaune a yankunan karkara.

“Muna kiran gwamnati da babbar murya da ta fito ta taimakawa ‘yan uwan mu makiyaya a wayar musu da kai akan wannan cutukan da suka bulla a kasar nan, sannan akwai cutar da ta ke damun dabbobi ma wacce ta shigo yanzu daga kasar Ghana”.

“Muna kira ga mai girma gwamnan jihar Kano Engineer Abba Kabir Yusuf, da ya taimaka ya sanya hannu a fadakar da ‘yan uwan mu fulani musamman wadanda ke jeji, domin da yawan su basu san wannan cutar ba”. Inji Jajere.

Alhaji Abubakar Muhammad Jajere, ya kuma yi kira ga mambobin kungiyar cewa duk wanda sabuwar wannan cutar yaga ta kama Dabbar sa guda to ya hanzarta ware Mata guri tare da tuntubar likitocin dabbobi domin a duba masa ita gudun kar wasu ma su kara kamuwa da cutar.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here