Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya cire sunan Dr. Ibrahim Yusuf Ngoshe daga cikin jerin wadanda ya ke son nadawa a matsayin kwamishinoninsa. A wata wasika da ya aike zuwa majalisar dokokin jihar Borno a yammacin ranar Juma’a, 28 ga watan Yuli, Gwamna Zulum ya bukaci yan majalisa da su cire sunan Yusuf Ngoshe daga cikin jerin kwamishinonin da ya aike masu.
Kakakin gwamnan, Malam Isa Gusau wanda ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya saki a ranar Asabar, 29 ga watan Yuli, ya yi bayanin cewa da wannan, adadin kwamishinonin da aka zaba ya ragu daga 18 zuwa 17. Sai dai kuma, Malam Gusau bai bayyana ainahin dalilin cire sunan Ngoshe ba amma ya ce za a gabatar da karin bayani kan lamarin idan bukatar hakan ya taso.
A ranar Juma’a, 28 ga watan Yuli ne Gwamna Zulum ya aike sunayen mutane 18 majalisar dokokin jihar domin tantancesu da kuma tabbatar da su a matsayin kwamishinoninsa.