Rundunar ‘Yan Sanda Tace Ta Gano Makamai Da Aka Boye A Ofisoshin Wasu Jam’iyun Siyasa

022a0000 0aff 0242 55f4 08dadd4a9e75 w650 r1 s
022a0000 0aff 0242 55f4 08dadd4a9e75 w650 r1 s

Kwamishinan ‘yan sanda a jihar Sakkwato Muhammad Usaini Gumel, yace sun samu labarin ana tara makaman ne inda suka kai samame suka kama makamai a ofisoshin jam’iyun APC da PDP na karamar hukumar Isa.

Yace makaman sun hada da adduna, sanduna, bindigar gargajiya ta harba ruga da sauran nau’o’in makamai.

To sai dai Muryar Amurka ta tuntubi kakakin jam’iyun da aka kama makaman a ofisoshin su, sun ce ba su da masaniyar haka.

Wannan na zuwa ne lokacin da rundunar sojin Najeriya ta ce tayi shiri na taimakawa a gudanar da zabe cikin lumana.

Tuni jama’ar yankunan da ke fama da matsalar rashin tsaro su ka nuna fargaba abin da kan iya faruwa lokutan zabe.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here