Gwamnatin tarayya ta ayyana ranar Litinin 3 ga watan Oktoba a matsayin ranar hutu domin bikin cikar kasar shekaru 62 da samun ‘yancin kan Najeriya.
Ministan harkokin cikin gida Alhaji Rauf Aregbesola ne ya sanar da hakan a wata sanarwa da ya fitar kuma aka rabawa manema labarai.
Cikin wata sanarwa ta hannun babban sakataren ma’aikatar, Dr Shuaib Belgore ya sanyawa hannu.
Ministan ya taya ‘yan Najeriya murnar bikin tare da ba da tabbacin aniyar gwamnati na tinkarar kalubalen da al’ummar kasar ke fuskanta da kuma sanya walwala a zukatan ‘yan Najeriya.
“Duniya na fama da matsalolin tattalin arziki da tsaro wadanda kuma suka shafi al’ummarmu kai tsaye.
Aregbesola ya nanata kudirin gwamnati na hada kan kasashe da kuma ganin kasa Najeriya ta samu cigaba.
Ministan daganan ya hori ‘yan Najeriya da su yi amfani da wannan damar wajen yin tunani kan kalubalen da al’ummar kasar ke fuskanta da kuma rawar da za su iya takawa wajen magance su.
Ministan ya kuma bukaci ‘yan Najeriya da su guji tashe-tashen hankula kuma su kasance masu lura da fannin tsaro, sannan su kai rahoton duk wani mutum ko wani abu da suke da alaka da su ga hukumar tsaro mafi kusa ta hanyar N-Alert.













































