Gwamnatin jihar Yobe ta soke lasisin makarantu masu zaman kan su

mai mala buni
mai mala buni

Gwamnatin jihar Yobe soke lasisin dukkan makarantu masu zaman kan su dake fadin jihar, tare da umartar duk mamallaka makrantun wadanda zasu iya bin sabbin dokokin da aka bullo da su kan su je su kara sabunta lasisin su.

Kazalika gwamnatin tace daga yanzu harkokin gudanawar makarantun dole ne su dace da na makarantun gwamnati.

Karanta wannan: Gwamnatin tarayya ta sake yin alkawarin kammala titin Abuja zuwa Kaduna a wannan Shekara

Kwamishinan ilimi na Jihar Dakta Muhammad Sani Idris, ne ya bayyana hakan ya yin wata ganawa da mamallaka makarantun ranar Alhamis a Kwalejin hadaka ta ‘Yan mata dake Damaturu.

Ya kara da cewa babu wata makaranta mai zaman kanta da za ta ci gaba da gudanar da ayyukanta ba tare da lasisi ba.

Karanta wannan: Gwamnatin Kano ta Kwace lasisin dukkan makarantu masu zaman kansu a fadin jihar 

Dakta Muhammad yace gwamnatin jihjar Yobe ta dauki matakan tafiyar da harkokin ilimi yadda ya kamata a jihar, la’khari da yadda wasu makarantun masu zaman kan su ke yin abubuwan da suka saba da dabi’un al’ummar Jihar.

Wasu daga cikin mamallaka makarantun da suka yi Magana da manema labarai jim kadan bayan kammala taron, sun ce zaman ya zo dai-dai lokacin da ya dace.

Sun kuma shawarci gwamnatin jihar da ta yi duk shirye-shiryen da suka kamata don ganin ba’a sha wahala ba wajen yin lasisin.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here