Gwamnatin tarayya ta sake yin alkawarin kammala aikin titin Abuja zuwa Kaduna nan karshen shekarar nan ta 2024.
Idan za’a iya tunawa dai gwamnatin ta sha yin alkawarin kammala titin a lokuta da dama, tun bayan da aka bada kwangilar gina shi a ranar 20 ga watan Disambar 2018.
A watan Oktoban 2022 ne tsohon karamin ministan ayyuka na kasa Umar El-Yakub, yace za’a kammala aikin titin Kaduna zuwa Abuja da kuma titin Zariya zuwa Kano, a farkon shekarar 2023.
Karanta wannan: Jami’an EFCC suna gudanar da bincike a babban ofishin Dangote hada-hadar kudaden kasashen waj
Kazalika shima tsohon ministan ayyuka da gidaje Babatunde Fashola, a watan Aprilun 2023, yace gwamnatin tarayya ta gaza cika alkawarin kammala aikin titin a 2022, amma za ta kammala shi a 2023.
Haka kuma da yake jawabi a wajen wani taron masu ruwa da tsaki ranar Alhamis a Abuja, ministan ayyuka David Umahi, ya bada tabbacin cewa ma’aikatar za ta magance duk kan matsalilin yan kwangila domin kammala ayyukan da ake yi nan da karshen 2024.
Karanta wannan: Mutum 2 sun mutu a hatsarin da tawagar Mataimakin Gwamnan Sokoto ta yi
Yanzu haka dai aikin sake gina titunan Abuja zuwa Kaduna da kuma Zariya zuwa Kano, yana hannun kamfanin Julius Berger, wanda shirin PDFI na gwamnatin tarayya ke kula da aikin.