Maitamakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima ya ce yana neman afuwar al’ummar Musulmi bisa wasu kalamai da ya yi game da zaben shugabannin Majalisar Dokokin Tarayya.
A cewar Mataimakin Shugaban Kasar, ba a fahimci maganar a muhallinta ba, kuma ba shi da wata manufa na bata sunan addininsa.
Sanata Kashim a tattaunawarsa da BBC ya ce ya yi wadannan kalamai ne saboda maslahar Najeriya, ganin cewa suna da wasu bayanan sirri da bai dace ya fito bainar jama’a yana bayani a kansu ba.
Sannan yadda lamura ke tafiya a Najeriya a wannan lokaci, dole shugabanni su fito su ja hankali domin wanzuwar kasar baki-daya.
Kalaman Shettima a cikin makon jiya sun haifar da zazzafar muhawara musamman a shafukan sada zumunta, inda aka rika sukar Mataimakin Shugaban Kasar.
Sai dai Kashim Shettima ya ce shi Musulmi ne na hakika domin zuri’arsu sun shafe tsawon dubban shekaru a kan tafarkin addinin.
Sannan duk wanda bai ji dadin kalamansa ba, ya yi hakuri a yafe masa, ba shi da niyyar muzanta wa addini.
“Ni dan Adam ne kuma ajizi don haka ina neman afuwar al’umma da Ubagijina.”
Kashim Shettima ya tunasar da cewa shi dan malamai ne kuma jikan malamai, don haka ba shi da niyyar muzantawa wani bangare na addinin kasar.