London: Jami’an hukumar shige da fice sun tsare Peter Obi na tsawon sa’a

Peter Obi new
Peter Obi new

A ranar Juma’ar da ta gabata ne dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour Party Mista Peter Obi, wanda ake zargin jami’an shige da fice na Burtaniya sun tsare shi a Landan.

An ce an tsare Obi na tsawon sa’o’i, kuma jami’an sun yi masa tambayoyi, bayan da jirginsa na British Airways ya sauka a filin jirgin sama na Heathrow da safiyar Juma’a.

Farfesa Chinyere Okunna, kwararriya a sashin aikin jarida kuma shugabar jami’ar Paul Awka, wanda kuma aminiyar Obi ce ta bayyana hakan a safiyar Laraba.

Okunna, wadda ta yi aiki tare da Obi a matsayin kwamishiyar yada labarai, kwamishinar tsare-tsare na tattalin arziki da kuma mai kula da abokan huldar raya kasa ta ce Obi wanda na zaune cikin mutunci a Burtaniya ta bayyana ra’ayinta game da halin da ya shiga.

Okunna ta ce: “Ina tsammanin ya gaya mani duk wannan a asirce. Kayi Hakuri Mai girma Obi, saboda ‘karya’ wannan sirrin, amma Tarihi ya nuna, kuma ba zan iya yin shiru ba.

“A gaskiya ban san ya fita daga kasar ba, har sai da aka yi masa murnar kasancewarsa a Cocin Landan

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here