Shugaban kwamitin amintattu na jam’iyyar PDP, Walid Jibrin, ya ce rashin adalci ne dan takarar shugaban kasa da kuma shugaban jam’iyyar na kasa su fito daga yanki daya.
Jibrin, ya bayyana hakan ne ranar Lahadi yayinda a cikin shirin Siyasa na gidan Talabijin na Channels.
Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP da Iyorchia Ayu shugaban jam’iyyar na kasa, da Walid Jibrin, shugaban kwamitin amintattu na jami’ar duk ‘yan yankin Arewa ne.
Jibrin ya ce har yanzu kwamitin koli na kasa, da kwamitin zartarwa na jam’iyyar a matakin kasa ba su shirya gudanar da taronsu ba, saboda suna jiran rahoton kwamitocin da aka kafa domin sasanta ’yan jami’ar da aka batawa.
Jibrin ya ce idan ta kama Shima da kansa zai yi murabus daga matsayinsa domin zaman lafiya ya wanzu a jam’iyyar.
Jam’iyyar dai ta fada cikin rikici ne tun bayan kammala zaben fidda gwani na shugaban kasa a watan Mayu.
Wike ya yi takarar tikitin takarar shugaban kasa amma ya sha kaye a hannun tsohon mataimakin shugaban kasar.
Rikicin ya kara kamari ne bayan da Atiku Abubakar ya nada Ifeanyi Okowa, gwamnan Delta a matsayin abokin takararsa a zaben shugaban kasa na Shekarar 2023.
Bayan sanarwar, wasu masu ruwa da tsaki na jam’iyyar sun bayyana damuwarsu kan yadda Abubakar ya yi watsi da Wike.
Rarrabuwar jam’iyyar ta kara ta’azzara ne bayan Atiku Abubakar ya yi hira da gidan Talabijin na Arise, inda ya bayyana dalilinsa na yin watsi da Wike.
Bayan tattaunawar be Kuma Wike ya mayar da martani, inda ya zargi dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar da yin “karya”.
Abubakar dai yana ta kokarin sasantawa da Wike amma har yanzu ba a samu ci gaban da ake bukata ba.
A makon da ya gabata, wata tawaga mai mutane uku da ya kafa ta gana da tawagar Wike a Rivers.
Rahotanni sun ce gwamnan Rivers na neman Ayu ya yi murabus a matsayin wani sharadi na tattaunawar domin samun zaman lafiya a Jam’iyyar.













































