Gwamnatin Kano za ta fara gurfanar da masu cin zarafin mata a makarantu a gaban kotu

WhatsApp Image 2025 04 16 at 09.14.45 750x430

Gwamnatin jihar Kano ta sha alwashin daukar kwararan matakai kan duk wani malami ko ma’aikacin makaranta da aka samu da laifin lalata da dalibai, inda ta bayyana cewa masu laifin za su fuskanci fushin doka.

Bayanin hakan ya fito ne a ranar Talata ta bakin babban mataimaki na musamman ga gwamna Abba Kabir Yusuf kan harkokin dalibai, Ibrahim Ma’ajiyi Sumaila, yayin wani taron masu ruwa da tsaki da cibiyar wayar da kan al’umma ta kasa (CAJA) ta shirya kan hanyoyin magance yawaitar cin zarafin mata a makarantun.

Sumaila ya ci gaba da cewa, “A matsayinta na kasar Musulunci Kano ba za ta nade hannunta tana kallon yadda ‘ya’yanmu mata ke fuskantar cin zarafi da wulakanci ba, duk malamin da ya kuskura ya ci zarafin daliba za a kore shi a gurfanar da shi ba tare da bata lokaci ba”.

Sumaila ya bayyana goyon bayan gwamnatin jihar ga kungiyoyi masu zaman kansu da ke jagorantar shawarwari da kawo sauyi a fannin.

Karin karatu: Wasu ƴan asalin Kano 2 sun mutu a ramin hakar ma’adinai a Neja

SolaceBase ta ruwaito cewa taron, wanda ya hada dalibai da kwararru kan harkokin yada labarai da dai sauransu, shine kaddamar da wani shiri na tsawon watanni shida da CAJA ta yi da nufin dakile cin zarafi ta hanyar tsara tsare-tsare a matakin hukumomi.

A nasa bangaren, Babban Darakta na CAJA, Kabiru Sa’id Dakata, ya ce an yi shirin ne don samar da manufofin cikin gida a manyan makarantun gaba da sakandire.

Ya koka da yadda yawancin wadanda abin ya shafa ke shan wahala ta hanyar jan bakinsu su yi shiru, inda wasu ke daina karatu ko kuma sun kasa yin karatu saboda sun ki yarda da bukatun malaman da suka yi lalata da su.

Barista Maryam Ahmad Abubakar, wacce ta gabatar da kasida kan fahimtar cin zarafi a fagen ilimi, ta bayyana aikin a matsayin duk wata dabi’ar jima’i da ba a so ba—na magana, ko na zahiri, ko kuma na hankali—wanda ke haifar da sauyin yanayi.

Ta jaddada bukatar wayar da kan ma’aikata da dalibai kan iyakoki, inda ta bayyana muhimmancin koyarwar tarbiyya da na addini wajen rage irin wadannan matsaloli.

Daga cikin dabarun da aka gabatar akwai: aiwatar da tsauraran hukunce-hukunce, sabunta shekarun shiga aiki, da shigar da koyarwar ɗabi’a cikin manhajojin karatu na gama gari.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here