Bayan cire tallafin wutar lantarki farashin wuta na iya karuwa a Najeriya

NEPA, cire, tallafi, wuta, lantarki, karuwa, farashi, najeriya
Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta ce zai yi wuya a ci gaba da bayar da tallafin wutar lantarki a kasar, kalaman Ministan wutar lantarki Adebayo Adelabu a wani...

Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta ce zai yi wuya a ci gaba da bayar da tallafin wutar lantarki a kasar, kalaman Ministan wutar lantarki Adebayo Adelabu a wani taron manema labarai a Abuja.

Ministan ya bayyana cewa bashin da ake bin kamfanonin samar da wutar lantarkin kasar wato (GenCos) da kamfanonin iskar gas (GasCos) ya haura Naira Tiriliyan 3.

Karanta wannan: PSC ta tantance masu neman aikin ‘Yan Sanda da za suyi CBT

Ministan ya tabbatar da cewa suna bin kamfanonin da ke samar da wutar lantarki bashin Naira Tiriliyan 1.3, wanda kashi 60 cikin 100 na bashin masu samar da iskar gas ne.

Ministan ya bayyana cewa, sun gaji bashi daga gwamnatocin da suka gabata kafin 2014, ga kamfanonin iskar gas na dala biliyan 1.3; a halin yanzu kusan Naira tiriliyan biyu.

Karanta wannan: Najeriya na kan tsini – Sultan Sa’ad

Adelabu ya jadada cewa suna aiki a karkashin kasa don tabbatar da cewa sun warware wadannan batutuwa tare da biyan wadannan basussuka ta hanyar samar da kudi ko sayar da kadarori.

Ministan, ya ce kasashe irin su Ghana da Togo da Jamhuriyar Benin suna biyan kudin wutar lantarki fiye da Najeriya, yana mai cewa gwamnati ba za ta iya ci gaba da bayar da tallafin wutar lantarki ba.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here