Gwamnatin tarayya dana jihohin Najeriya 36 na nazari akan bukatar kafa rundunonin ‘yan sandan jihohi.
Hakan ya biyo bayan wani taron gaggawa daya gudana yau Alhamis tsakanin Shugaba Bola Tinubu da gwamnonin kasar a fadarsa ta Aso Rock.
Karanta wannan: Bayan cire tallafin wutar lantarki farashin wuta na iya karuwa a Najeriya
Taron na zuwa ne sakamakon karuwar matsalolin hauhawar farashin kayan abinci da tsadar rayuwa da rashin tsaro a fadin Najeriya a ‘yan kwanakin baya-bayan nan.
A jawabinsa ga manema labarai na fadar gwamnatin jim kadan bayan kammala taron, Ministan yada labarai da wayar da kan al’umma Muhammad Idris.
Ya bayyana cewar har yanzu ba’a kai ga cimma matsaya akan batun ba, amma komai zai fito fili idan aka samu karin tattaunawa tsakanin masu ruwa da tsakin.