
Fitaccen ɗan kasuwar nan Alhaji Aminu Dantata da ke jihar Kano a Najeriya, ya bayyana cewa tsarin Firaminista da wasu ‘yan majalisun tarayya ke ƙoƙarin tabbatarwa shine ne yafi zama alheri ga kasa Najeriya.
Dantata, ya bayyana haka ne a lokacin da wasu ‘yan majalisar wakilan Najeriya ƙarƙashin jagorancin shugaban marasa rinjaye, Kingsley Chinda, suka kai masa ziyarar neman shawara a gidansa da ke Kano a ranar Alhamis.
Karanta wannan: Bayan cire tallafin wutar lantarki farashin wuta na iya karuwa a Najeriya
Aminu, ya kuma bayyana godiyarsa bisa ziyarar da suka kawo gidansa, “Hakika naji dadin haka a gare ni, tare da yiwa wannan babban yunƙuri na ku fatan alkhairi da nasara”.
Ya kara da cewa, “Tsarin Firaminista ya fi kyau ga kasar nan domin yana da sauki fiye da kima ba kamar irin na shugaban ƙasa mai cikakken iko da yake da tsada sosai ba, musamman ga kasa kamar Najeriya” Inji shi.
Karanta wannan: Tinubu ya gana da gwamnoni kan taɓarɓarewar tattalin arziƙi da tsaro
A karshe ya bayyana cewa, “Ina fatan za ku sami haɗin kan abokan aikinku kuma ina rokon Allah ya ba ku hikima ya kuma yi muku jagora don cimma wannan kyakkyawan aiki na taimakon kasar nan domin ta haka ne za’a iya samun abinda ake da bukata anan gaba”.
Idan za’a iya tunawa dai wasu ‘yan majalisu 60 sun nuna goyon bayansu kan wannan yunƙuri na mayar da Najeriya tsarin Firaminista kamar yadda ƙasar ta ke a jamhuriya ta farko da kuma kafin ƙasar ta sami yancin kai wanda suke ganin shine mafi sauki da dacewa.












































