Yan Bindiga Sun Kashe Mutane 4, Sun Raunata 4 tar da watsar da mutane 5 da sukai garkuwa da su a Kaduna 

Nigeria Kidnappings Bandits deputy
Nigeria Kidnappings Bandits deputy

‘Yan bindiga sun kashe mutum 4, sun raunata 4, sun yi watsi da mutum 5 da su kai garkuwa da su a Kaduna.

‘Yan bindiga sun kashe mutane hudu tare da raunata wasu hudu a Uguwan Dankali da ke karamar hukumar Zariya a jihar Kaduna a ranar Juma’a, kamar yadda kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna, ASP Mansir Hassan, ya bayyana a ranar Lahadi.

Ya kara da cewa, a lokacin da aka kai musu daukin gaggawa, tawagar hadin guiwa ta ‘yan sanda da sojoji da kuma rundunar hadin guiwa ta farar hula sun shiga farautar ‘yan bindigar.

Hassan ya kara da cewa, a fafatawar da aka yi, ‘yan bindigar sun yi watsi da mutane biyar da suka rigaya suka yi garkuwa da su.

“An ceto wadanda abin ya shafa nan take aka kai su asibiti tare da wadanda suka jikkata,” inji shi.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here