Mu Yi Sadaukarwa Domin Ci Gaba Da Hadin Kan Nijeriya – Sarkin Gwandu

Muhammadu Iliyasu Bashar 750x430

Sarkin Gwandu na Kebbi, Muhammadu Iliyasu-Bashar, ya bukaci ‘yan Najeriya da su nuna kishin kasa don bunkasa zaman lafiya da hadin kai a kasar.

Ya bayyana haka ne a yayin wani liyafa da aka shirya don karrama mataimakin shugaban jami’ar Fatakwal, Farfesa Georgewill Owunary, a fadarsa da ke Birnin Kebbi ranar Asabar.

Shugaban Majalisar Sarakunan Kebbi ya ce “kasar nan tamu ce, don haka dole mu dauki kanmu a matsayin ‘yan uwa. Najeriya babbar kasa ce kuma tana dauke da abubuwa da yawa, dole ne mu sadaukar da kai don ganin ta kasance daya.”

Tun da farko, Onuwary ya yaba da wannan karimcin da sarkin ya yi, inda ya bayyana hakan a matsayin wani abin alfahari da bai taba samu ba a rayuwarsa.

 

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here