Kamfanin X ya amince zai biya tsoffin ma’aikatansa na Ghana

1708271895184

Kamfanin X, da a baya aka fi sani da Twitter ya amince zai biya tsoffin ma’aikatansa da suka yi aiki a ofishinsa da ke Ghana, bayan lokaci mai tsawo da aka ɗauka ana shari’a kan batun.

Ma’aitan kamfanin da dama ne aka sallama daga bakin aiki bayan da attajirin ɗan kasuwar nan Elon Musk ya sayi kamfanin a shekarar 2022.

Sai dai kamfanin bai bayyana adadin kuɗin da kowane ma’aikacin zai samu ba, da kuma lokacin da zai biya kuɗin.

To amma lauyoyin ma’aikatan sun ce sun cimma yarjejeniyar biyan ma’aikatan kuɗaɗe sallamarsu, tare da kuɗin guzuri ga ma’aikatan da ba ‘yan Ghana ba, don su samu abin da za su koma ƙasashensu.

A cikin sanarwar da lauyoyin suka fitar, sun ce dokokin Ghana sun yi tanadin cewar dole a tabbatar ma’aikatan da aka sallama daga aiki, ba su faɗa cikin matsin rayuwa ba.

Kamfan sada zumuntar ya gaza yin aiki da umarnin da ofishin shugaban ƙwadagon Ghana ya ba shi, na bai wa ma’aikatan kuɗin sallamar, kamar yadda dokokin ƙwadagon ƙasar suka tanada.

Lauyoyin sun ce tsoffin ma’aikatan na cikin murna da farin ciki da sabuwar yarjejeniyar da aka cimma da kamfanin.

Ma’aikata da dama ne dai suka kaɗu da matakin kamfanin na X ya ɗauka na rufe ofishinsa guda ɗaya tilo a Afirka tare da sallamar ma’aikatansa a 2022.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here