Tsohon Shugaban Jami’ar Bayero Ta Kano, Farfesa Umar, Ya Rasu

FB IMG 1675144012959
FB IMG 1675144012959

Fitaccen likita kuma tsohon shugaban jami’ar Bayero ta Kano, BUK, Farfesa Ibrahim Umar ya riga mu gidan gaskiya. Dansa, Farouk Ibrahim Umar ya tabbatar da rasuwar mahaifinsa, a ranar Litinin yana mai cewa za a yi jana’izarsa a Kofar Kudu misalin karfe 10 na safiyar Talata.

Marigayin, wanda ya jagoranci BUK tsakanin 1979 da 1986, shine shugaban jami’ar na uku. Shine dan Najeriya na farko da ya fara koyar da Physics a jami’ar a shekarar 1976. A hirarsa na karshe da Daily Trust a 2017, marigayin ya yi waiwaye inda ya bayyana mukamai daban-daban da ya rike a kasa da waje, ciki har da wakiltar Najeriya Kwamitin Makamashi na Duniya daga 1990 kuma yana cikin tawagar da ta tsara kundin tsarin mulkin kasa na 1979.

Yana cikin tawagar Najeriya da ta tafi taron Hukumar Kula da Makamashin Nukiliya na Kasa da Kasa, IAEA, daga 1989 kuma aka nada shi shugaba Hukumar Makamashi na Najeriya a 1989. Ya yi aiki a matsayin shugaban kwamitin IAEA daga 2000-2001 kuma a 2004 shine direkta na cibiyar binciken makamashi da horaswa, inda na’urar bincike na nukiliya na farko a kasar ya ke. Mukamin da aka sani ya rike na karshe shine a 2007, lokacin da aka nada shi a kwamitin bada shawarwari na kasa da kasa kan makamashi wanda ake sabunta shi.

A hirar, ya shawarci yan Najeriya ‘su tabbatar sun zabi mutane wadanda za su yi wa kasa aiki ba don za su bawa mutane kudi ba’ a matsayin daya cikin hanyar warware kallubalen da ke damun kasar.

Dakaci karin bayani …

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here