Hukumar Tsaron Farin Kaya ta DSS da sanyin safiyar Litinin ta ce jami’anta sun kama wasu jami’an bankuna da ke cuwa-cuwar sabbin takardun kudi.
DSS ta ce ta kama jami’an ne a wasu manyan garuruwa da ke Jihohin kano da Legas da Ribas da kuma Babban Birnin Tarayya Abuja.
Kakakin hukumar, Peter Afunanya ne ya tabbatar da kamun ranar Litinin.
Ya ce daukar matakin ya zama wajibi ne la’akari da yadda mutane ke yi wa harkar rarraba takardun da Babban Bankin Najeriya ke yi zagon kasa.
Muna tafe da karin bayani…













































