Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da tashar wutar lantarki mai amfani da hasken rana, mai karfin megawatt 10 a karamar hukumar Kumbotso dake jihar Kano, ranar Litinin.

Jaridar solacebase ta rawaitu cewa an shafe tsawon shekaru biyu ana gudanar da aikin, sakamakon tsai ku da annobar cutar corona ta kawo, wanda tashar itace babbar wutar lantarki mai amfani da hasken a Najeriya.

Hukumar ta Nigeria Sovereign Investment Authority (NSIA) ta ce tashar zata bada wuta ga kamfanonin dake challawa, wanda hakan zai rage matsalar wuta da suke fama da ita, sanan kuma ta samar da aikin yi tare da kawo sauki kan sarrafa abubuwa.

Shugaban hukumar ta Nigeria Sovereign Investment Authority, Aminu Umar Sadiq, ya ce anyi amfani da hicta 24 wajan gina tashar.

