Najeriya Ta Tafka Asarar Tiriliyan 3 Sanadiyyar Ambaliya A Bara – Gwamnati

Sadiya Faruq
Sadiya Faruq

Ministar Jinkai da Walwalar Jama’a, Hajiya Sadiya Umar Farouk ta ce jimlar asarar da Najeriya ta tafka a sanadiyyar ambaliyar ruwa a shekarar 2022 ta haura ta Naira tiriliyan uku.

Ta ce an tattara alkaluman ne daga farkon shekarar zuwa ranar 25 ga watan Nuwamba.

Da take jawabi a karshen mako a Abuja yayin gabatar da wani rahoto kan ambaliyar, ta ce wuraren da barnar ta shafa sun hada da gidaje da sauran gine-gine da ma gonaki.

Sai dai ta ce duk da haka, barnar ba ta kai wacce aka fuskanta a shekara ta 2012 ba.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here