Gwamnan Kano ya dakatar da Manajan Daraktan KASCO

gwamna, cututtuka, kula, amincewar, kafa, cibiyar
Majalisar dokokin jihar Kano ta samu takarda daga gwamna Alhaji Abba Kabir Yusuf bisa neman majalisar ta duba tare da amincewa da bukatar kafa cibiyar yaki...
Gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusif ya bayar da umarnin dakatar da Manajan Daraktan Kamfanin Samar da Aikin Gona na Kano (KASCO) Dakta Tukur Dayyabu Minjibir.
An dakatar da Manajan Darakta bisa zarginsa da hannu a sayar da hatsin da bai dace ba na Gwamnatin Jihar Kano.
An umarci Dakta Dayyabu da ya mika al’amuran kamfanin ga babban jami’i nan take har sai an kammala bincike.

Jaridar SOLACEBASE ta ruwaito cewa Gwamnan ya bada umarnin dakatarwar ne a wata takarda mai dauke da kwanan watan 12 ga watan Satumba 2023 wanda sakataren gwamnatin jihar Kano Dr. Abdullahi Baffa Bichi ya mika.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here