
Gwamnan jihar kano Abba Kabir Yusuf ya amunce da nada dan wansa, Ahmad A. Yusuf, a matsayin sakataren hukumar raya al’adu da tarihi ta jihar Kano.
Ahmad Yusuf dan wan gwamnan Kano ne wanda ya tasu a gidan Abba Kabir Yusuf tun yana karami kuma yake amfani da sunan gwamnan, wanda har ma gwamnan Kano ke kiransa da babban dansa.
Idon zaku iya tunawa dai a ranar da yake karbar shidar cin zabe da hukumar INEC ta bashi ya sha alwashin bazai sa wani daga cikin iyalin sa a cikin gwamnantinsa ba.
Kwatsam sai ga wata sanarwa wacce babban skataren yada labaran gwamnan Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fifatar a ranar Lahadi wacce ta ke dauke da sabbabin su nayen dade naden da gwaman yai, wanda sunan Dan wan gwaman na cikin sunayen.












































