Filato: An Sanya Dokar Hana Fita Ta Awa 24 A Mangu

Dokar hana fita
Dokar hana fita

A sakamakon zaman dardar da ake ciki a Karamar Hukumar Mangu da ke Jihar Filato. Shugaban Karamar Hukumar, Markus Artu, ya sanya dokar hana zirga–zirga ta tsawon awa 24.

Shugaban ya sanya dokar ce a wata sanarwa da ya fitar mai dauke da sanya hanunsa., ranar Litinin.

Sanarwar ta yi bayanin cewa dokar ta kunshi hana zirga-zirgar dukkan ababen hawa na awa 24 a yankin, har sai abin da hali ya yi.

“Ba a son ganin kowa yana zirga-zirga a yankin, sai dai jami’an tsaro ko kuma wadanda aikinsu ya zama wajibi ga al’umma,” in ji sanarwar.

Matakin sanya dokar na zuwa ne bayan da aka sami wasu munanan hare-hare kwanakin baya.

Hare-haren dai sun yi sanadin asarar rayukan sama da mutum 150 da dukiyoyi masu tarin yawa.

(Aminiya)

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here