Tsohon shugaban kamfanin Man Fetur na Ƙasa (NNPCL), Mele Kyari, ya bayyana a ofishin jukumar yaƙi da cin H’hanci da rashawa (EFCC) a Abuja da misalin ƙarfe 2:15 na rana a ranar Laraba.
An gayyace shi domin amsa tambayoyi kan harkokin kuɗi da na fasaha da suka shafi lokacin da yake jagorancin kamfanin.
Tun da farko, EFCC ta saka sunansa cikin jerin masu sa ido saboda binciken gyaran matatun mai da darajarsa ta kai dala biliyan 7.2.
Haka kuma, wata kotu a Abuja ta bayar da umarnin rufe wasu asusun banki guda hudu da ake dangantawa da shi bisa zargin aikata almundahana.












































