INEC ta amince da David Mark a matsayin shugaban jam’iyyar ADC 

ADC Mark Aregbe 750x430

Hukumar Zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta amince da sabon shugabancin jam’iyyar adawa ta African Democratic Congress (ADC) ƙarƙashin jagorancin tsohon shugaban majalisar dattawa, Sanata David Bonaventure Mark, a matsayin shugaban jam’iyyar na ƙasa.

A ranar Laraba a Abuja, INEC ta sabunta bayanan jam’iyyar a shafinta na intanet, inda ta lissafa sabbin shugabannin jam’iyyar, abin da ya tabbatar da kawo ƙarshen rikicin shugabanci da ya daɗe a cikin ADC.

Karin labari: Dokar Zaɓe ta keɓance INEC daga hukunta ƴan siyasa kan fara Kamfen da wuri – Mahmood Yakubu

A cewar hukumar, sabon kwamitin zartarwa na ADC yana ƙarƙashin jagorancin Sanata Mark a matsayin shugaban ƙasa, yayin da tsohon gwamnan Jihar Osun, Ogbeni Rauf Aregbesola, ya zama sakataren ƙasa.

Sauran shugabannin sun haɗa da Dr. Mani Ibrahim Ahmad a matsayin ma’ajin ƙasa, Akibu Dalhatu a matsayin sakataren kuɗi na ƙasa, da kuma tsohon gwamnan Jihar Edo, Farfesa Oserheimen Aigberaodion Osunbor, a matsayin mai ba da shawara kan harkokin shari’a na jam’iyyar.

 

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here