Borno ta tabbatar da kashe zaki a karamar hukumar Konduga

The Lion killed in Malari village of Konduga LG
The Lion killed in Malari village of Konduga LG

Daraktan gandun daji da namun daji na ma’aikatar muhalli ta jihar Borno Mista Peter Ayuba ya tabbatar da kisan wani zaki da mafarauta suka yi a karamar hukumar Konduga.

Ayuba, wanda ya zanta da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya, NAN, kan lamarin a ranar Talata a Maiduguri, ya ce mai yiwuwa zakin ya kauce daga dajin Waza da ke makwabciyar kasar Kamaru.

“Muna da irin wannan lamarin na Giwaye daga gandun daji suna shiga kauyukan karamar hukumar Kala-Balge.

“Akwai kuma wani lamari na wasu kuraye da suka kashe wani mutum a daji a karamar hukumar Kaga.

“Rashin mutane a wasu yankunan karkara na shekaru da yawa ya mayar da yawancin gonaki zuwa gandun daji,” in ji Ayuba.

Ayuba ya bukaci al’ummomin da aka sake tsugunar da su da su yi taka-tsan-tsan da kuma lura, inda ya nuna cewa zakin da aka kashe a ranar Lahadi zai iya sa wasu zakunan su dauki fansa.

Shima da yake magana kan lamarin, jami’in yada labarai na karamar hukumar Konduga, Malam Asheikh Chabbol, ya ce zakin ya kori wasu manoman rani a kauyen Malari wadanda sai da suka gayyato mafarauta domin gudanar da aikin.

“Mafarauta sun yi ma zakin, wanda ya raunata biyu daga cikinsu kafin a kashe shi.

“Mafarautan da suka jikkata suna karbar magani yayin da aka kai gawar zakin zuwa ma’aikatar muhalli,” in ji Chabbol.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here