Majalisar wakilai ta kuduri aniyar gudanar da bincike kan lamarin da ya sa jirgin kasa da ke jigilar fasinjoji daga Legas zuwa Ibadan ya rasa mai a tsakiyar hanyar.
Hakan ya biyo bayan amincewa da kudirin gaggawa da dan majalisar wakilai Ndudi Elumelu, shugaban marasa rinjaye na majalisar ya gabatar a ranar Talata a Abuja.
A cikin kudirin nasa, Elumelu ya ce ya kamata hukumar kula da layin dogo ta Najeriya (NRC) ta kasance tana saukakawa masu safarar manyan kayayyaki ta hanyar samar da tsari mai kyau.
Dan majalisar ya lura cewa ana yawan samun matsaloli wanda hakan ke janyo barazanar kai hare-hare a jiragen na kasa.
“Wani abin bakin ciki kuma ya faru ne a ranar 11 ga watan Maris, inda wani jirgin kasa da ke jigilar fasinjoji da kayayyaki daga Legas zuwa Ibadan ya tsaya tsakiyar daji saboda karewar man fetur.
“Hakan ya sake jefa rayuwar matafiya ‘yan Najeriya da ba su ji ba ba su gani ba a wannan tafiya cikin hadari,” inji shi.
Dan majalisar ya ce akwai bukatar hukumar ta NRC ta inganta ayyukan da suka shafi sayar da tikiti da kuma sauran bangarori da ake samun matsala.
A cewarsa, hakan na durkusar da kudaden shigar da gwamnati ke samu wanda ya hana biyan bashin da aka yi niyya da kuma zagon kasa ga tattalin arziki.
Ya kuma bayyana cewa da Mista Fidelis Okhiria, Manajan Darakta na NRC, ya bayar ba wai kawai abin dariya ba ne, amma yana nuna gazawa wajen gudanar da daidaitaccen bincike na yau da kullun.
Majalisar ta yanke shawarar kafa wani kwamiti na wucin gadi wanda zai yi bincike kan matsayin NRC da gazawarta sannan ya kai rahoto ga majalisar cikin makonni hudu.













































