Kotu ta ƙi bayar da belin waɗanda ake zargi da hannu a harin cocin Owo

Owo Church Suspects

Babbar kotun tarayya da ke Abuja ta ƙi bayar da belin mutum biyar da ake tuhuma da shirya harin da aka kai a cocin Katolika ta Owo dake jihar Ondo, kamar yadda gidan talabijin na Channels ya ruwaito.

Hukumar tsaro ta farin kaya DSS ta gabatar da mutum biyar ɗin ne a gaban alƙalin Kotun, Emeka Nwite, a ranar 11 ga Agusta, 2025, kan zargin hannunsu a harin da aka kai cocin a ranar 5 ga Yunin 2022.

Mutanen da ake tuhuma za su fuskanci shari’a kan harin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutum sama da 40 tare da jikkata fiye da 100.

A lokacin sauraron ƙarar, Alƙalin Kotun, ya ƙi amincewa da belin, inda ya bayyana cewa laifin da ake tuhumarsu da shi yana da nauyi sosai.

Alkalin ya kuma jaddada yiwuwar cewa waɗanda ake tuhuma za su iya tsoratar da shaidu su rinjayi shari’a, ko su tsere idan aka sake su.

Alƙalin ya kuma amince da hujjojin DSS, wadda ta ce akwai hujjoji masu ƙarfi a kan waɗanda ake tuhuma.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here