Wasu ‘yan bindiga dauke da makamai sun kashe dan sanda 1 da wasu mutane 6 a wani hari da suka kai a hedikwatar sashin ‘yan sanda da ke karamar hukumar Zurmi a jihar Zamfara.
Haka kuma shaguna da dama ‘yan ta’addan sun kona su.
‘Yan bindigar sun mamaye garin da yammacin Lahadin da ta gabata, inda suka je ofishin ‘yan sanda kai tsaye suka bude wuta kan ‘yan sandan da ke bakin aiki.
Karanta wannan: Aminu Dantata ya ce tsarin firaminista ne yafi dacewa ga Najeriya
Wasu mazauna yankin sun ce harin na baya-bayan nan na ramuwar gayya ne bayan da ‘yan banga suka kashe wasu ‘yan bindiga biyu a garin Zurmi.
Wannan dai shi ne karo na biyu cikin kasa da watanni uku da ‘yan bindiga ke kai hari a garin na Zurmi.
Harin na karshe wanda ya dauki tsawon wasu kwanaki ya tilastawa wasu kungiyoyi masu zaman kansu da ke ba da aikin jinya kyauta a yankin rufe ayyukansu domin kare lafiyar ma’aikatan.
Hukumomin ‘yan sanda a Zamfara ta bakin mai magana da yawun rundunar ASP Yazid Abubakar ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya kara da cewa an tura karin sojoji yankin kuma an samu zaman lafiya.
Karanta wannan: ‘Yan Sanda Sun Kama Masu Buga Jabun Kudi 12 A Gombe
Rundunar ‘yan sandan ta sha alwashin bin diddigin wadanda suka aikata wannan mugunyar aikin.
Wannan harin da aka kai a garin Zurmi, daya daga cikin kananan hukumomin da ke da sansanonin ‘yan fashi da makami, na zuwa ne ‘yan kwanaki bayan da majalisar dattawa ta gayyaci hafsoshin tsaro kan matsalar rashin tsaro a fadin kasar nan.
Da kuma kusan makonni hudu da gwamnatin jihar Zamfara ta kaddamar da na ta jami’an tsaro mai suna Community Protection Guards don taimakawa wajen magance ƴan fashi da garkuwa da mutane.