Kakakin Kremlin, Dmitry Peskov ya ce ana ci gaba da gudanar da bincike kan mutuwar Navalny amma har zuwa safiyar Litinin babu wani sakamako har yanzu.
Binciken ya ƙara da cewa ana gudanar da binciken bisa ga dokar Rasha.
Karanta wannan: ‘Yan Bindiga sun kai hari ofishin ‘Yan Sanda tare da kashe mutum 7 a Zamfara
Kakakin ya kuma ɗauki wani lokaci wajen kare shugaban kasar Rasha Vladimir Putin bisa zargin da shugabannin kasashen yammacin duniya ke yi masa na cewa shi ne ke da alhakin mutuwar Navalny.
Peskov ya ce “Mun yi la’akari da cewa ba za mu yarda da irin waɗannan maganganun banƙyama ba, haƙiƙa wadannan kalamai ba za su iya kawo barna ga shugaban kasarmu ba.”