Tinubu ya mayar da shugaban NTA da aka sauke

NTA New 750x430

Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya bayar da umarnin mayar da tsohon shugaban hukumar Talbijin na Ƙasa NTA da aka sauke kwanakin baya Salihu Abdullahi Dembos sakamakon sauye-sauyen da aka gudanar a hukumar.

Cikin wata sanarwa da kakakin shugaban ƙasa Bayo Onanuga ya fitar ya ce Dembos wanda Shugaba Tinubu ya naɗa a 2023 – a yanzu zai dawo domin kammala wa’adin mulkinsa na shekara uku.

A ƴan kwanakin nan ne aka sanar da sauke Dembos sakamakon wasu sauye-sauye da aka gudanar da hukumar.

Sauke shi ya janyo zazzafar muharawa da suka musamman daga yankin arewacin ƙasar, inda Salihu Abdullahi Dembos ya fito.

Haka ma shugaban ƙasa ya bayar da umarnin maido da Mista Ayo Adewuyi a matsayin babban daraktan sashen labarai na NTA, domin shi ma ya ƙara wa’adinsa na shekara uku da zai ƙare a 2027.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here