Majalisar wakilai ta musanta yunkurin tsige shugabanta Tajudeen Abbas

Reps Speaker Abbass 720x430

Majalisar wakilai ta sake jaddada amincewarta da shugabancin kakakin majalisar, Tajudeen Abbas, inda ta ce babu wani shiri na tsige shi.

Mataimakin mai magana da yawun majalisar wakilai, Philip Agbese ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Talata a Abuja.

Agbese, wanda ya yaba da nagartar shugabancin kakakin, ya ce Abbas yana ci gaba da rike kyawawan halaye da mutunta abokan aiki.

Da yake bayyana kakakin a matsayin jagora abin koyi, Agbese ya ce ya nuna jagoranci wajen inganta jin dadin ‘yan majalisa da ci gaban mazabu.

Karanta: Wike da wasu jiga-jigai sun zayyana sharuddan gudanar da ingantaccen taron jam’iyyar PDP na ƙasa

Da yake yin watsi da rahoton da kafafen yada labarai na baya-bayan nan suka fitar kan zargin shirin yin fito-na-fito da shugaban majalisar, bayan dawowa daga hutu, Agbese ya bayyana rahotannin a matsayin hasashe kuma da gangan aka yi don haifar da sabani a zauren majalisar.

Ya yi nuni da cewa, korafe-korafen da ake samu kan daukar ma’aikata a Majalisar Dokoki ta kasa, ko dai ta hanyar bata gari ne ko kuma ba da labarin karya.

Agbese ya fayyace cewa hukumar kula da masu yiwa kasa hidima ta kasa ce ta dauki ma’aikata, wata kungiya ce mai zaman kanta ba ta shugaban majalisar ko kuma shugabannin majalisa ta 10 ba.

Sai dai ya ce a matsayinsa na shugaba ya kafa kwamitoci na musamman guda biyu domin duba batutuwan.

Agbese ya ce daya daga cikin kwamitocin ne zai kasance karkashin mataimakin kakakin majalisar Rt. Hon. Benjamin Kalu da sauransu karkashin jagorancin tsohon mataimakin kakakin majalisar wakilai ta tara, Rt. Hon Idris Wase.

Karin karatu: Na yi dacen zabar ka a matsayin mataimakin shugaban kasa – Tinubu ya shaida wa Shettima @59

Agbese, ya kuma baiwa ‘yan Najeriya tabbacin mayar da hankali kan al’amuran kasa, musamman aikin gyaran kundin tsarin mulkin kasar da ake yi, rashin tsaro, sauye-sauyen tattalin arziki da aiwatar da kasafin kudi da dai sauransu.

Ya bukaci kafafen yada labarai da su rika tantance gaskiya kafin a yada labari don guje wa rahotannin da za su kawo cikas ga kyakkyawar alakar aiki a tsakanin ‘yan majalisa da kuma tsakanin majalisar dokoki da al’ummar Najeriya.

Agbese ya tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa majalisar, karkashin Abbas, ta ci gaba da mai da hankali wajen samar da dokoki da suka shafi jama’a da kuma jagoranci mai cikakken iko wanda zai magance kalubalen yau da kullum na ‘yan kasa a fadin kasar nan.(NAN)

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here