Jami’an Tsaro: Sun cafke wadanda suka haddasa kashe-kashen Jihar Filato

Jami'an tsaro, cafke, kashe-kashen, filato
Jami'an tsaro a Jihar Filato sun cafke mutanen da ake zargi sun kitsa kashe-kashen kwanan nan a kananan hukumomin Mangu, Bokkos da Barikin Ladi...

 

Rundunar ’Yan Sandan Jihar, ta ce mutum 17 ne suka shiga hannun jami’anta kan harin ranar jajiberen Kirsimeti a kananan hukumomin uku inda aka kashe mutane kimanin 100.Da yake gabatar da su ga manema labarai, Mataimakin Sufeto-Janar mai kula da Shiya ta 4, Ebony Eyibio, ya ce tara daga cikin wadanda ake zargin an kama su ne kan zargin hannunsu a kashe-kashen Mangu, ragowar takwas din kuma kan zargin kashe-kashe a Bokkos da Barikin Ladi.

Karanta wannan: Gwamnatin jihar Kebbi ta kori wasu hakimai 3 bisa zargin rashin da’a

Eyibio wanda kakakin rundunar, DSP Alabo Alfred, ya wakilta ya ce, “Ranar Alhamis da misalin karfe 10 na dare aka tsegunta mana game da wasu da ke shirin kai hari a yankin Ntam da kuma ASTC da ke Karamar Hukumar Mangu.

“Shi ne zaratan jami’anmu suka kai samame suka dakile yunkurin kai harin” Inji shi.

Ya kara da cewa, “Jami’anmu sun dakile yunkurin masu kona gidaje da wuraren ibada a yankin Panyam da taimakon wasu dattawan yankin.

 

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here