Kotun sauraron ƙararrakin zaɓen shugaban kasa ta kori ƙarar da jam’iyyar APM ta shigar gaban ta

BREAKING 750x430
BREAKING 750x430

Kotun sauraren kararrakin zaben shugaban kasa da ke zamanta a Abuja ta yi watsi da zargin nadin Kashim Shettima da jam’iyyar APC ta yi a matsayin wanda zai wa Tinubu mataimaki ba bisa ka’ida ba.

Kotun ta ce al’amurran da suka shafi rashin cancantar wani lamari ne gabanin zabe inda ta kara da cewa mutum daya tilo da ya isa ya kafa wani mataki na wannan dabi’a shi ne wanda ya shiga zaben fidda gwani.

Jam’iyyar Allied Peoples Movement (APM) ta bukaci kotun da ta soke mataimakin shugaban kasar, inda ta ce a lokacin da aka tsayar da shi takarar mataimakin shugaban kasa bai janye takararsa ba a matsayin dan takarar Sanatan Borno ta tsakiya a jam’iyyar APC.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here